unfoldingWord 16 - Masu Kubutarwa
Pääpiirteet: Judges 1-3; 6-8; 1 Samuel 1-10
Käsikirjoituksen numero: 1216
Kieli: Hausa
Yleisö: General
Tarkoitus: Evangelism; Teaching
Features: Bible Stories; Paraphrase Scripture
Tila: Approved
Käsikirjoitukset ovat perusohjeita muille kielille kääntämiseen ja tallentamiseen. Niitä tulee mukauttaa tarpeen mukaan, jotta ne olisivat ymmärrettäviä ja merkityksellisiä kullekin kulttuurille ja kielelle. Jotkut käytetyt termit ja käsitteet saattavat vaatia lisäselvitystä tai jopa korvata tai jättää kokonaan pois.
Käsikirjoitusteksti
Bayan mutuwan Joshuwa, Isra'ilawa sun yi wa Allah rashin biyayya da basu kori sauran Kan'aniyawa ko su kiyaye shari'un Allah ba. Isra'ilawa sun shiga bautan allolin Kan'aniyawa sun manta da Yahweh, Allah na gaskiya. Isra'ilawa ba su da sarki, don haka kowa na yin abin da ya ga dama.
Domin rashin biyayyan da Isra'ilawa suka ci gaba da yi wa Allah, Ya hore su ta wurin ba makiyansu su yi nasara akan su. Makiyan nan sun saci abubbuwa da yawa daga Isra'ilawa, sun hallakar da mallakansu, sun kuma kashe su da yawa. Bayan shekaru da yawa na yi wa Allah rashin biyayya da kuma shan tsanani daga makiya, Isra'ilawa sun tuba sun roki Allah Ya kubutar da su.
Sa'annan Allah ya tanada masu mai kubutarwa wanda ya kubutar da su daga hannun makiyan su, ta haka ne ya kawo salama a kasar. Amma kuma mutanen sun manta da Allah sun koma ga bautar gumaku. Saboda haka Allah Ya yarda Midiyanawa, makiyan su na kurkusa su ka sami nasara akansu.
Midiyanawa kuwa suka dauki dukkan amfanin gonar Isra'ilawa na shekaru bakwai. Isra'ilawa kuwa suka tsorata; suka buya a koguna don kada Midiyanawa su same su. Daga karshe kuwa, sun yi kuka ga Allah domin Ya cece su.
Wata rana, wani mutumin Isra'ila mai suna Gidiyon yana bugun hatsi a asirce don kada Midiyanawa su gani su sace. Mala'ikan Yahweh kuwa ya zo wurin Gidiyon ya ce, "Allah na tare da kai, ya kai babban jarumi. Jeka ka ceci Isra'ila daga hannun Midiyanawa."
Mahaifin Gidiyon kuwa na da bagadi da ke na gumaka. Allah kuwa Ya fada wa Gidiyon ya rushe bagadin. Amma don tsoron mutane, Gidiyon ya jira zuwa maraice. Sa'annan ya rushe bagadin, ya rugurguje shi. Ya kuma gina sabuwar bagadi ga Allah kusa da inda bagadin gumakan nan yake a da, anan ya mika hadaya ga Allah akan ta.
Kashegari mutane sun gano cewa wani ya yaga ya kuma rushe bagadin, sai sun husata. Sun nufa gidan su Gidiyon domin su kashe shi, amma mahaifin Gidiyon yace, "Me ya sa kuna kokarin ku taimaki allahnku? Indai shi allah ne, ya kare kansa mana!" Fadinsa haka, mutanen basu kashe Gidiyon kuma ba.
Midiyanawa kuwa suka kuma zuwa don yin sata daga Isra'ilawa. Yawansu ya fi gaban a kirga. Gidiyon kuwa yayi kira ga Isra'ilawa su yake su. Gidiyon ya nemi alamu biyu daga wurin Allah don samun tabbacin Allah zai more shi don ya ceci Isra'ila.
Alama ta farko, Gidiyon ya shimfida fatar tunkiya a kasa, ya roki Allah Ya bar rabar safiya ya sauka akan fatan tunkiyar kadai ban da a kasa. Allah yayi haka. Dare na biye, yayi roko yana so kasa ne kawai da raba, fatan tunkiya kuma a bushe. Allah Ya sake yin haka. Wadannan alamu biyu sun tabbatar wa Gidiyon da cewa Allah zai yi amfani da shi don ceton Isra'ila daga Midiyanawa.
Sojojin Isra'ila 32,000 suka zo wurin Gidiyon, amma Allah Ya gaya masa cewa sun yi yawa. Saboda haka Gidiyon ya komar da 22,000 gida da ke tsoron yaki. Allah Ya kuma ce wa Gidiyon, har yanzu mutanen na da yawa. Saboda haka Gidiyon ya komar da dukkan su gida, sai sojoji 300 ne kawai ya bari.
A wannan dare kuwa, Allah Ya gaya wa Gidiyon, "Jeka sansanin Midiyanawa, in ka ji abin da suka ce, ba zaka ji tsoro kuma ba." A cikin daren, Gidiyon ya nufi sansanin, ya ji wani sojan Midiyanawa na fada wa abokin sa mafarkin da yayi. Abokin mutumin ya ce, "Ma'anar wannan mafarkin shi ne, mayakan Gidiyon zasu ci mayakan Midiyanawa da yaki!" Da Gidiyon ya ji haka, yayi sujada ga Allah.
Da Gidiyon ya komo wurin sojojin sa, ya ba kowannen su kaho, tukunyar kasa, da kuma tocila. Sun kewaye sansani inda sojojin Midiyanawa na sharan barci. Sojojin Gidiyon 300 suna da tociloli cikin tukwane, a yadda Midiyanawa ba za su iya ganin hasken tocilolin ba.
Sa'annan, sojojin Gidiyon duka suka farfashe tukwanen su a lokaci daya, nan da nan kuma wutan tocilolin ya bayyana. Suka busa kaho suka yi ihu suna cewa, "Takobin Yahweh da na Gidiyon!"
Allah Ya kawo rudani ga Midiyanawa, sun fara kai wa juna hari suna kashe junan su. Nan da nan, an kirawo sauran Isra'ilawa daga gidajen su domin su taimaka wurin koran Midiyanawa. Sun kashe masu yawan su, sun kuma kori sauran, sun fitar da su daga kasar Isra'ilawa. Midiyanawa 120,000 ne suka mutu a ranar. Allah ya ceci Isra'ila.
Mutanen na so su nada Gidiyon sarkin su. Gidiyon bai yarda masu ba, amma ya roki zobba na zinariya da kowannen su ya dauka daga wurin Midiyanawa. Mutanen sun ba Gidiyon zinariya masu yawan gaske.
Gidiyon kuwa yayi amfani da zinariyar wurin yin tufafi na musamman, irin da babban firist ke sa. Amma mutane sun fara wa tuffan sujada kamar ga gumaka. Saboda haka Allah Ya hori Isra'ila kuma, domin suna bauta wa gumaku. Allah Ya bar makiyan su su sami nasara akansu. A karshe su ka roki Allah Ya taimake su, Allah kuma Ya aika masu wani mai kubutarwa.
Wannan yanayi ya maimaita kansa sau da dama: Isra'ilawa za su yi zunubi, Allah kuma Ya hore su, za su tuba, Allah kuma Ya aika mai kubutarwa ya cece su. Shekaru da dama Allah na aikan masu kubutarwa da ke ceton Isra'ilawa daga makiyan su.
A karshe, mutanen sun roki Allah Ya ba su sarki kamar yadda sauran al'ummai ke da shi. Suna neman sarki wanda ke da tsayi da kuma karfi, wanda kuma zai jagorance su zuwa yaki. Allah bai ji dadin wannan rokon na su ba, amma Ya ba su sarki irin da suke so.