Good News

Good News

Eskema: Short Bible stories from Genesis through the ascension. How to become a follower of Jesus. 40 sections. It has a picture book to go along with the recording.

Gidoi zenbakia: 395

Hizkuntza: Hausa

Gaia: Sin and Satan (Temptation, Deliverance, Light/Darkness, Sin, disobedience, Satan (the devil)); Christ (Jesus, Our Substitute, Resurrection of Jesus, Son of God, Saviour of Sinful Men, Birth of Christ, Ascension, Sacrifice / Atonement, Death of Christ, Life of Christ); Eternal life (Salvation, Eternal / everlasting life, Broad & Narrow Ways); Character of God (Love of God, Holy Spirit, Grace and Mercy, Nature, character of God, Word of God (the Bible), Power of God / Jesus); Living as a Christian (Fruit of the Spirit, Prayer, petition, New Nature, Worship, Witnessing, Church, Christianity, Second Birth, Obedience, No other gods, idols, Peace with God, Leaving old way, begin new way, Forgiveness, Faith, trust, believe in Jesus, Peace (between men), Children of God, Family, relationships, Spiritual Life, Christian values); Life event (Death); Bible timeline (Creation, Law of God, End Time, Second Coming, Gospel, Good News, People of God); Problems (Materialism, Evil Spirits, demons, Fear, Problems, troubles, worries)

Publikoa: General

Estiloa: Monolog

Generoa: Bible Stories & Teac

Helburua: Evangelism

Bibliako aipua: Extensive

Egoera: Approved

Gidoiak beste hizkuntzetara itzultzeko eta grabatzeko oinarrizko jarraibideak dira. Beharrezkoa den moduan egokitu behar dira kultura eta hizkuntza ezberdin bakoitzerako ulergarriak eta garrantzitsuak izan daitezen. Baliteke erabilitako termino eta kontzeptu batzuk azalpen gehiago behar izatea edo guztiz ordezkatu edo ezabatzea ere.

Gidoiaren Testua

Gabtarwa

Gabtarwa

Barkanku abokai ( gaisuwa ta al'ada). Ku zo ku saurari wannan labari mai dadi. Ku dubi littafin nan mai dauke da hoto ku kuma saurara da kyau. Ku tuna, idan kun ji wannan kara, ku dubi hoto na gaba. (bada alama).

HOTO NA 1: A Cikin Farko

HOTO NA 1: A Cikin Farko

Farawa 1:1-4; Zabura 90:2

A cikin farko ruwa da kasa da haske babu su. Ba komai sai Allah na gaskiya cikin sama.Allah ya ce bari haske ya kasance, nan da nan sai haske ya kasance. Allah kuma ya raba haske da duhu. Ya ce da haske yini, duhu kuma ya ce da shi dare. Ta wurin maganarsa ya raba tsakanin ruwa da kasa.ne kadai. Allah nagari ne yana mulki akan abu duka. Kamar yadda kuka gani a cikin hoto na farko, Allah ya halicci duniya ya kuma umurci haske ya haskaka. Ya yi hasken rana domin ya yi mulkin rana, wata kuma ya yi mulkin dare.

HOTO NA 2: Kalmar Allah

HOTO NA 2: Kalmar Allah

Ishaya 45:18-19; Ibraniyawa 4:12

Littafin da ke cikin hoton nan ana kiransa Baibul (Littafi Mai Tsarki). Kalmar Allah ce kuma tana fada mana game da Allah da dukan hanyoyinsa. Allah na kaunar dukan mutane. Mun rabu da Allah, amma kuma Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana wata hanya guda daya da zamu sulhuntu da shi. Wadannan labarin na gaskiya daga cikin Littafi Mai Tsarki suke.

HOTO NA 3: Halitta

HOTO NA 3: Halitta

Farawa 1:1-25

Allah ya yi komai ta wurin maganarsa. Ya yi komai da kyau, ya yi kasa da duwatsu, da ruwa da koguna. Daga nan sai ya halicci dukan abubuwa masu rai, kifi a cikin ruwa, tsunsaye a sama da dukan dabbobi. Allah kuwa ya ga komai da ya halitta na da kyau.

HOTO NA 4: Adamu da Hauwa’u

HOTO NA 4: Adamu da Hauwa’u

Farawa 1:26-31, 2:7 - 3:24

Daga nan sai Allah ya halicci mutum na farko da mace ta farko. Sai ya kira su Adamu da Hauwa'u. Ya ba su iko akan dukan abin da ya halitta. Abokan Allah ne su. Ya ce ma Adamu kuna iya cin dukan 'ya'yan itace da ke cikin gonar, amma kada ku ci daga cikin itace na tsakiyar gonar watau na sanin nagarta da mugunta. In kun ci lalle za ku mutu. Amma akwai wani mugun mayaudari, ana kiran sa Shaidan. Ya yi wa Hawa'u karya cewa, idan kun ci wannan itacen, ba za ku mutu ba. Za ku zama kamar Allah. Za ku san nagarta da mugunta. Hawa'u ta yi wa Allah rashin biyyaya, ta tsinka 'ya'yan itacen ta ci ta kuma ba wa mijin ta, shi kuma ya karba ya ci. Dukan su sun yi wa Allah rashin biyyaya. A gefen hagu na hoto zaku gansu sun yi wa Allah rashin biyayya ta wurin cin 'ya'yan itacen nan da aka dokace su koda su ci. Sun yi zunubi sun kuma karya zumuntarsu da Allah. A hannun dama na hoto, kun ga yadda Allah ya hori Adamu da Hauwa'u, ta wurin korar su daga cikin gonar. Tun daga wannan lokacin, dole dukan mutane su yi aiki tukuru kafin su sami abincin da za su ci. Haka kuma sun dandana shan azaba da cuta da mutuwa.

HOTO NA 5: Kayinu da Habila

HOTO NA 5: Kayinu da Habila

Farawa 4:1-16; Romawa 3:23

Adamu da Hauwa'u na da 'ya'ya maza guda biyu, Kayinu da Habila. Sai Kayinu na jin kishin Habila don Habila ya mika hadaya mara aibi ga Allah. Allah ya karbi hadayar Habila amma bai karbi hadayar Kayinu ba don ya mika mai aibi. Don haka Kayinu ya ji kishin Habila, wata rana sai ya kashe shi. Allah ya hori Kayinu saboda zunubin sa kamar yadda ya hori Adamu da Hauwa'u. Mu zuriyar Adamu ne, da haka kuma mu ma mun yi zunubi. Zunubi na raba mutum da Allah. Mun cancanci horo domin zunubanmu.

HOTO NA 6: Jirgin Nuhu

HOTO NA 6: Jirgin Nuhu

Farawa 6:1-22; 2 Bitrus 3:9

Tsararraki (shekaru) masu yawa suka wuce kuma an sami zuriyar Adamu masu yawa. Haka kuma, wadannan mutane sun yi zunubi sun yiwa Allah rashin biyayya. Zunuban mutane ya kasaita. Amma Akwai mutum daya kadai da ya ke kaunar Allah. Sunansa Nuhu. Allah ya ce wa Nuhu ya sassaka babban jirgi. Allah zai ceci Nuhu da iyalinsa a cikin jirgin. Nuhu ya yi wa'azin adalcin Allah, a duk shekaru da ya yi yana sassaka jirgin. Mutane ba su gaskanta da gargadin Nuhu ba. Sun ki juyawa ga barin mugayen hanyoyin su don samun tsira daga ruwan tufana.

HOTO NA 7: Ruwan tufanna

HOTO NA 7: Ruwan tufanna

Farawa 7:1-24

Nuhu ya sa dabbobi da tsuntsaye iri iri a cikin jirgin kamar yadda Allah ya fada masa. Nuhu tare da matarsa, da 'ya'yansu uku tare da matayensu ma sun shiga cikin jirgin.

Daga nan sai Allah ya rufe kofar jirgin. Sai Allah ya sauko da ruwa mai karfi; ruwa ya yi ta bulbulowa daga kasa, ya rufe duniya. Sai ya zama da latti wani ya ce zai tuba ya sami ceto, amma Nuhu da iyalinsa suna cikin jirgin lafiya lau. Amma wadanda ke waje sun hallaka. Nuhu ya tsira saboda ya gaskanta da Allah ya kuma yi biyayya da shi.

HOTO NA 8: Ibrahim da Saratu da Ishaku

HOTO NA 8: Ibrahim da Saratu da Ishaku

Farawa 9:7-19, 12:1-7, 17:18, 18:1-15, 21:1-7

Tsara da yawa ta wuce (shekaru) kuma zuriyar Nuhu ta zama kabilu masu yawa. Ibrahim mutum ne da yake kaunar Allah yana kuma yi masa biyayya. Allah ya alkawarta wa Ibrahim cewa tsatsonsa zasu zama babban zuriya. Ibrahim da matatasa Saratu basu da 'ya'ya amma sun gaskanta alkawarin Allah. Wannan hoto ya nuna cewa sun sami Da (yaro) a tsufarsu kuma sun ba shi suna Ishaku. Ibrahim da Ishaku ne kakanin kakanin Yesu Kristi, wanda ya zo ya ceci duniya.

HOTO NA 9: Musa da shari’ar Allah

HOTO NA 9: Musa da shari’ar Allah

Farawa 19:1-25, 34:37-32

Zuriyar Ibrahim ta zama babban zuriya da ake kira da suna Isra'ilawa. Musa na zuriyar Ibrahim ne wanda kuma yana tsoron Allah ya kuma gaskanta da shi. Wata rana, sai Allah ya kirayi Musa a kan dutse ya ba shi dokokin da zai koyawa mutane. Wannan hoto yana nuna Musa yana saukowa daga kan dutse tare da dokokin Allah rubuce akan dutse. Allah na son dukan mutane su yi biyayya da dokokinsa.

HOTO NA 10: Dokoki guda goma

HOTO NA 10: Dokoki guda goma

Fitowa 20:1-17

Ga wadansu dokoki da Allah ya ba Musa. Sun koya mana kauna da yi wa Allah na gaskiya biyyaya. Da farko mu dubi hoto na sama, mun ga cewa ba zamu bautawa wadansu alloli ba ko wadansu siffofin dabbobi ko wadansu abubuwa ba. Dole ne mu yi wa Allah sujada shi kadai. A hoto na gaba kuma zamu ga uba dauwa da yara suna bautawa Allah tare. Ya kamata mutane su ajiye rana guda daya a cikin kowanne mako domin yin sujada. Na gaba, dole 'y'aya su yiwa iyayensu biyayya su ga darajar su kuma.

A hoto na gefen hagu na kasa, dokar Allah ta ce kada mu yi kisan kai. A na gaba, kada mu dauki matar wani, kada mu yi zina. A hoto na karshe, ba za mu yi sata ba ko mu yi marmarin satar kayan wani. Allah ya umurcemu mu kiyaye dokokin sa.

HOTO NA 11: Yin hadaya domin zunubi

HOTO NA 11: Yin hadaya domin zunubi

Levitikus 4:27-28, 32-35; Yohana 1:2a

A zamanin da, idan mutum ya karya dokar Allah, dole ne ya bada hadayar rago ga Allah. Ragon zai mutu a maimakon wanda ya yi laifin. Ragon wata alama ce ta Dan Allah, wato Ubangiji Yesu Kristi. Yesu zai zo ya kuma mutu a matsayin hadaya ga Allah domin dukan mutanen duniya. "Duba, ga Dan rago na Allah mai daukan zunuban duniya". Yesu ya zama hadaya domin zunubanmu ta wurin mutuwa akan giciye. Ka ba da gaskiya ga Yesu Kristi, ka furta zunubanka. Ka tuba, ta haka kuma Allah zai gafarce ka.

HOTO NA 12: An yi alkawarin Mai Ceto

HOTO NA 12: An yi alkawarin Mai Ceto

Luka1:26-38; Matta 1:18-25

Yanzu, bari mu ji yadda aka haifi Yesu Kristi. Da dadewa, Allah ya alkawarta aiko da Mai Ceto. A hoto hannun hagu, zaka ga malai'ka wanda ya sauko daga sama zuwa ga wata budurwa mai suna Maryamu. Maryamu wanda Yusufu ke tashinta su yi aure. Ba ta taba sanin namiji ba. Malai'ka ya ce mata, "Ruhun Allah zai sauko maki kuma za ki yi ciki. Za ki kira jaririn Yesu Dan Allah". Kamar yadda ka gani a cikin hoto na hannun dama, malai'ka kuma ya bayyana ga Yusufu a cikin mafarki. Malai'ka yace, "Yusufu, kada ka ji tsoro, ka dauki Maryamu ta zama matarka. Juna biyun da take da shi daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne na Allah. Sunan jariri zai zama Yesu, ma'ana, Mai Ceto. Shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu". Sai Yusufu ya yi biyayya ga Allah, kuma bai taba sanin Maryamu ba har sai da ta haifi jaririn.

HOTO NA 13: Haihuwar Yesu

HOTO NA 13: Haihuwar Yesu

Luka 2:1-20

Dole Yusufu da Maryamu su tafi wani birni wanda ake kira Baitalami. Da suka isa wurin, babu wani masauki domin su. Duk gidaje sun cika babu sauran wuri, don haka ya zama dole su yi masauki a gidan dabbobi. A wannan wuri ne Maryamu ta haifi Danta Yesu. A wannan dare Mala'ika ya bayyana ga wasu makiyaya wadanda suke kiwon garken tumakinsu a kusa da inda aka haifi Yesu. Sai ya fada masu haihuwar da aka yi ta Yesu a Baitalami. Daga nan sai rundunan mala'iku suka bayyana a sararin sama suna yabon Allah. Makiyayan suka tafi su ga Mai Ceto.

HOTO NA 14: Yesu a matsayin malami

HOTO NA 14: Yesu a matsayin malami

Luka 2:39-52; Markus 6:30-34

A cikin hoto na gefen hagu mun ga Yesu lokacin da ya ke dan shekara 12. Yana yin magana akan Allah tare da malamai da shugabanin Isra'ilawa, suna sauraro yana yin tambayoyi. Sun yi mamakin girman saninsa na Allah. Hoto da yake a hannun dama ya nuna lokacin da Yesu ya yi girma ya zama babban mutum, yana koyawa mutane sanin Allah. Wadansu mutane sun gaskanta koyarwarsa kuma sun yi masa biyayya. Wadansu ba su gaskanta da shi ba, sun yi tsayayya da shi. Allah na son mu gaskanta mu kuma bi Yesu.

HOTO NA 15: Ayyukan al’ajibai na Yesu

HOTO NA 15: Ayyukan al’ajibai na Yesu

Markus 8:2-26, 5:21-24, 35-43, 6:45-52

Wadannan hotuna sun nuna manyan ikokin da Yesu yake da su na yin wadannan al'ajiban. A hannun hagu, Yesu ya taba mutumin nan da aka haife shi makaho, kuma yana gani! Hoto na tsakiya na nuna Yesu yana tadda wani yaron da ya mutu, a yayin da uban yaro da uwar suke kallo. Daga karshe, muna ganin Yesu na tafiya akan saman ruwa. Yana tafiya zuwa wurin almajiransa wadanda suke cikin kwale- kwalen su. Ubangiji Yesu ya yi ayyukan mu'ujizai da yawa kamar wadannan domin ya nuna shi Dan Allah ne. Yesu zai taimakemu ma, ta wurin ikon ruhunsa.

HOTO NA 16: Yesu ya sha wuya

HOTO NA 16: Yesu ya sha wuya

Matta 27:1-2, 11-14, 26-31

Yesu yayi ayyukan ban al'ajabi kuma mutane da yawa sun bi shi. Yesu mai alheri ne, ya warkadda masu ciwo ya kuma koyar da hanyar Allah. Ya zo domin ya ceci batattu, mutane masu zunubi. Duk da haka, mugayen mutane sun tsane shi da ya ce, su masu zunubi ne. Shugabanin mutane na kishin Yesu ba su gaskanta cewa Yesu Dan Allah ba ne. Sun kama shi, sun yi masa karya sun kuma duke shi. Sun sa masa rawanin kaya, sun tofa masa yawu kuma sun yi masa ba'a. Amma Yesu bai guje su ba. Ya san abin da zai faru da shi. Ya kyale mugayen mutane su ji masa rauni su kuma kashe shi. Yesu ya zo domin ya mutu a matsayin hadaya ta Allah. Ya dauki laifi domin zunuban dukan mutane.

HOTO NA 17: An giciye Yesu

HOTO NA 17: An giciye Yesu

Markus 15:21-39; 1 Bitrus 2:21-24

Sojoji sun giciye Yesu a kan giciye, sun kafa giciyen a kasa, kuma sun rataye shi har sai da ya mutu. An giciye mafasa guda biyu tare da shi Yesu. A wancan zamani, al'ada ce a kashe barayi ta muguwar hanya. Amma Yesu bai yi wani laifi ba. Ya zamanto abin hadaya kuma mun cancanci mutuwa domin zunuban mu. Yesu ya karbi horon da yake namu ne. Idan mun furta zunubin mu kuma muka juyo da gaskiya daga zunuban mu Allah zai gafarce mu. Ka gaskata, ka karbi Yesu Kristi, zaka sami ceto.

HOTO NA 18: Tashi daga matattu

HOTO NA 18: Tashi daga matattu

Luka 23:50 - 24:9

Makiyan Yesu na tsammani sun hallaka shi, amma ba haka ba ne! Bayan da Yesu ya mutu akan giciye, sai abokansa suka ajiye gangar jikinsa a cikin kogo. Sai suka rufe bakin kogon da babban dutse. Kwana biyu ya wuce, a rana ta uku sai Yesu ya tashi daga matattu. Lokacin da wadansu mataye suka je wurin kabarin sai suka iske an mirginar da dutsen, kuma Yesu ba ya nan. Sai suka ga mala'iku guda biyu, suka fada cewa Yesu na da rai. " Ba ya nan. Ya tashi," In ji Mala'ikun. Sa'adda Yesu ya tashi daga matattu, sai ya nuna afili cewa shi ne Allah Dan ne. Har wa yau Yesu na da rai kuma ya fi Shaidan karfi, ya kuma fi mutuwa karfi.

HOTO NA 19: Toma ya gaskanta

HOTO NA 19: Toma ya gaskanta

Yohanna 20:19-31

Bayan Yesu ya tashi daga matattu, almajiransa da yawa sun gan shi, sun yi magana da shi, sun ci abinci tare da shi.

Toma, daya daga cikin almajiransa bai gaskanta cewa Yesu na da rai kuma ba. Sai ya ce, "Sai na ga ramin kusar da aka kafa masa, in sa yatsana a cikin ramin, in ba haka ba, ba zan gaskanta ba". Mun gani a cikin hoto cewa Yesu ya zo ya nuna wa Toma ramin kusar da aka kafa masa. Toma ya kauda shakkarsa. Sai ya fadi a gaban Yesu ya ce, "Ubangiji da Allah na". Sai Yesu ya ce, "Masu albarka ne wadanda ba su gan ni ba amma sun gaskanta".

HOTO NA 20: Hawan Yesu zuwa sama

HOTO NA 20: Hawan Yesu zuwa sama

Ayyukan Manzanni 1:1-11

Bayan kwana 40 da Yesu ya tashi daga matattu, ya bayyana ga mutane da yawa. Mutune da yawa sun gan shi da rai. Yanzu lokaci ya yi da Yesu zai koma wurin Uba a sama. Ya gama aikin da ya kawo shi a duniya. Yesu ya fadawa almajiransa su fada wa dukan mutane a ko'ina wannan labarin mai dadi. Almajirai suna duba har Yesu ya bar duniya ya hau zuwa sama. Mala'iku guda biyu cikin farin kaya suka bayyana suka fadawa almajirai cewa wata rana zai sake dawowa duniya, daga sama kamar yadda suka gan shi yana tafiya. Har sai wannan lokacin ya zo, Yesu yana sama a yanzu, yana shirya wuri a can sama domin dukan wadanda suka bada gaskiya suka kuma bi shi. A wannan lokacin, kai kuma fa? Ko zaka gaskanta ka bi Yesu? Ko kana shirye ka sadu da shi?

HOTO NA 21: Giciyen da ba shi da kome

HOTO NA 21: Giciyen da ba shi da kome

Yohanna 19:38-42; 1 Bitrus 3:18

Me yasa Yesu ya mutu akan giciye? Yesu ya mutu domin ya ceci masu zunubi daga horon zunubi. Yesu bai taba yin zunnubi ba, amma kuma ya mutu domin ya dauke zunubi da ya raba mu da Allah. Giciyen na tunashe mu cewa Yesu mara aibi ne (mai tsarki, mara zunubi) Dan ragon Allah. An mika shi hadaya domin mu. Idan mun bada gaskiya a cikin Yesu mun tuba mun bar zunubi, Allah zai gafarta mana zunuban mu. Yesu ya maishemu 'ya'yan Allah. Wadannan hotunan zasu taimake mu, mu gane abin da ake nufi na zama mai bin Yesu.

HOTO NA 22: Hanyoyi guda biyu

HOTO NA 22: Hanyoyi guda biyu

Irimiya 21:8; Matta 7:13-14

Yesu ya koyar cewa akwai hanyoyi guda biyu. Dukan mutane na kan hanya mai fadi wadda take kaiwa ga hallaka, cikin wutar jahannama. Dukanmu muna da halin zunubi da muka gada daga wurin Adamu. Yesu ya ce mu bi kunkuntar hanya wadda za ta kai mu ga Allah a cikin sama. Idan mutum ya gaskanta da Yesu a cikin wannan rayuwar, ya kuma bi shi zai sami rai na har abada. Zai bar bin hanya mai fadi zuwa cikin kunkuntar wadda ta ke kaiwa zuwa sama. Babu shari'a domin zunubi ga wadanda suke kan kunkuntar hanya. Ka yi zabe; idan ka shawarta zaka bi Yesu, ka iya magana da Allah a cikin addua'a kamar haka: "Ya Allah, na furta cewa ni mai zunubi ne. na gaskanta cewa Yesu ya mutu akan giciye domin ya biya hakkin zunubi na. Ka gafarce ni ka tsarkake zuciyata ka maida ni daya daga cikin iyalinka Yesu, kuma bayan mutuwa, ina so in zauna tare da kai a sama. Na gode ya Allah".

HOTO NA 23: ’Ya’yan Allah

HOTO NA 23: ’Ya’yan Allah

Yohanna 14:6, 3:16, 6:37-40

A cikin wannan hoto za ka ga Yesu na marabtar mutane daga kowacce kabila da kasa da harshe. Sun gaskanta da shi a yanzu kuma sun zama 'ya'yan Allah. Suna kan kunkuntar hanya wadda take kaiwa zuwa sama. 'Ya'yan Allah na nan kamar iyali, suna tattare wuri guda a cikin Ubangiji Yesu.

HOTO NA 24: Haihuwa na biyu

HOTO NA 24: Haihuwa na biyu

Yohanna 3:1-18; Romawa 8:9-17

Wata rana da dare, wani malamin addini, Nikodimus ya zo wurin Yesu domin ya koyi sanin Allah. Yesu ya fada masa cewa duk wanda ya ke so ya kasance a cikin iyalin Allah, yana bukatar sabon rai. Wannan na nan kamar sake maye haihuwa. Ba mu da ikon canza kanmu. Ruhu Mai Tsarki na Allah ne yake ba mu sabon rai idan mun gaskanta mun kuma bi Yesu, mun zama sabobbin mutane, mutanen Allah.

HOTO NA 25: Ruhu Mai Tsarki ya zo

HOTO NA 25: Ruhu Mai Tsarki ya zo

Ayyukan Manzanni 2:1-21, 37-39; Yohanna 14:15-27

Wadannan mutane, almajiran Yesu ne. Kafin Yesu ya koma zuwa sama ya alkawarta zai aiko masu da kyautar Ruhu Mai Tsarki. Kwana goma bayan Yesu ya koma sama wadannan almajirai suna tattare wuri guda. Nan da nan, sai Ruhu Mai Tsarki na Allah ya cika su duka kamar yadda Yesu ya alkawarta. Almajiran sun sami iko yin magana cikin harsuna daban daban domin su fadawa mutane abubuwan ban al'ajabi da Allah ya yi. Ruhu Mai Tsarki na Allah na zaune a cikin dukan masu bi na gaskiya, kuma yana ba su iko su kaunaci Yesu.

HOTO NA 26: Yin tafiya a cikin haske

HOTO NA 26: Yin tafiya a cikin haske

Yahana 3:19-21, 8:12,12:35-36,46

Kafin mutum ya gaskanta da Yesu, yana kama da mutumin da yake tafiya a cikin duhu. Yana tuntube ya fadi sau da dama saboda ba shi da hasken da zai jagorance shi. Idan mun yi bangaskiya cikin Yesu, zamu zama kamar mutumin da yake tafiya akan mikakkiyar hanya da rana! Yesu ya ce "Ni ne hasken duniya duk wanda ya bi ni, ba zai taba yin tafiya a cikin duhu ba". Allah yana bada Ruhu Mai Tsarki don ya yi ( taimako) ya koyawa dukan masu binsa hanyarsa ta rayuwa.

HOTO NA 27: Sabon mutum

HOTO NA 27: Sabon mutum

Afisawa 4:22-24; Galatiyawa 5:16-26

Mai bada gaskiya (krista) a cikin Yesu Kristi sabon mutum ne kuma yana yin biyayya da magannar Allah, yana godiya domin Yesu ya gafarta masa zunubansa. Mai bi ba ya yin zina, fada ko sata, ko bautar gumaka ko bauta wa sauran alloli ko ruhohi. Ruhu Mai Tsarki na ba mai bi ikon juyawa daga aikata abubuwa na mugunta ya kuma yi abubuwa masu kyau.

HOTO NA 28: Iyalin krista

HOTO NA 28: Iyalin krista

Afisawa 5:21-6:4; 1 Bitrus 3:1-9

Dubi wannan iyalin wadanda suke yin tafiya a cikin hanyar Allah. Mutumin na kaunar matarsa, matar kuma na yiwa mijin biyayya. Wannan ne abin da kalmar Allah ta umurta. Suna taimakon junansu, suna kuma tarbiyyar da yaransu su kaunaci Allah su kiyaye maganarsa. Dole iyalin krista su rika yin addu'a da yin tafiya tare da Allah.

HOTO NA 29: Ka kaunaci makiyinka

HOTO NA 29: Ka kaunaci makiyinka

Matta 5:43-44; Luka 10:25-37; 1 Yohana 3:14-18

Yesu ya koyawa mabiyansa su kaunaci dukan mutane, har ma da makwabtansu. Mu taimaki duk mai bukata, har ma da mutanen wasu kabilu. Yesu ya bada labarin wani mutum da yake tafiya zuwa wani gari. Mafasa suka auka masa suka bubuge shi. Wani mutum na wata kabila ya iske matafiyin a kwance ya taimaki mutumin nan saboda yana cikin bukata. Bai ce a biya shi wani kudi ba. Yesu ya fada mana mu rika aikata abubuwa nagari kamar wannan mutumin.

HOTO NA 30: Yesu ne mai iko shi kadai

HOTO NA 30: Yesu ne mai iko shi kadai

Matta 6:24; Ayukan mazanni 19:18-20; Zabura 115:1-8; Yohana 4:4

Wadannan mutanen suna kone gumakai da guraye. Suna dogara ga wadannan kafin su zuma masu bin Yesu. Amma ya zama dole masu bi su kawar da komai wato duk wani abin da ke na Shaidan, da mugayen ruhohi. Ubangiji na da iko fiye da Shaidan da mugayen ruhohi da gumakai (layun masu tsafi). Mu masu bi bai kamata mu ji tsoron Shaidan ba. Dole ne mu roki Allah shi kadai ya taimakemu ya tsare mu.

HOTO NA 31: Fitar da mugayen ruhohi

HOTO NA 31: Fitar da mugayen ruhohi

Markus 5:1-20; Ayyukan Manzanni 16:16-18

A wannan hoto mun ga mutumin da yake da mugayen ruhohi. Igiyoyi da sarkoki ba sa iya rike shi, saboda mugayen ruhohin (aljannu) da ke cikinsa na da karfi. Yesu ya umurci mugayen ruhohin nan su fita daga cikin mutumin kuma sun fita! Mutumin nan ya warke. Ya kuma tafi ya fadawa abokansa abin da Yesu ya yi masa. Ba za a taba kwatanta ikon Yesu da na mugayen ruhohi ba, dole mugayen ruhohi su yi wa Yesu biyayya. ZABI: Idan ka gaji da damuwa da mugayen ruhohi suke kawo maka, ka roki sauran masu bi su yi addu'a tare da kai. Ka roki Ubangiji Yesu Kristi mai iko ya kore su. Idan muna kaunar Yesu muna kuma yi masa biyayya, zai zauna a cikin mu. Ta wurin ikonsa zai tsare mu, kuma shaidan ba zai iya cutar mu ba.

HOTO NA 32: Gwaji

HOTO NA 32: Gwaji

Matta 6:24; Korintiyawa 10:1-14; Timothawus 6:3-12

Wannan hoto na nuna wani mai bi da ake gwada shi ya bar bin Yesu. Shaidan na son mu manta da Allah mu kuma rika yin tunanin kudi da kayayyaki da taba, aikin masha'a, da giya mai karfi akoyaushe. Shaidan ya ce wadannan abubuwan zasu sa mu ji dadi. Mai bi na iya yin tsayayya da Shadan idan ya dubi Yesu ya kuma bi shi.

HOTO NA 33: Idan muka yi zunubi

HOTO NA 33: Idan muka yi zunubi

Luka 15:11-32; 1 Yohana 1:7-9

Yesu ya bada wani labari kamar haka: "Wani yaro ya bar gida, ya tafi wata kasa mai nisa ya aikata wasu mugayen abubuwa masu yawa. Yayi kuka da kansa saboda zunubinsa kuma sai ya koma wurin ubansa. Ubansa yana kaunarsa sosai, sai ya karbe shi kuma". Wannan labarin na fada mana cewa idan mun yi zunubi, dole ne mu gane da zunubin mu, mu juyo mu bari zunubin. Saboda Allah na kaunarmu sosai, zai gafarta mana zunubinmu ya sake karbarmu kuma.

HOTO NA 34: Ciwo

HOTO NA 34: Ciwo

2 Sarakuna 20:5-7; 1 Bitrus 5:6-10; Yakubu 5:14-16

Wannan mutumin da matar na bakin ciki (damuwa) saboda yan'uwansu ba su da lafiya. Me mutanen Allah za su yi idan ba su da lafiya? Sai su yi addu'a, su gaskanta cewa Allah zai yi dukan abin da ya ga ya dace. Allah na warkar da wanda ba shi da lafiya in ya nufi yin haka ko kuma ya taimakeka ka sami magani mafi dacewa. Allah na kaunarmu yana kuma sarrafa duk wani abin da yake faruwa da 'ya'yansa. Allah na tsare mai bi daga Shaidan, don haka dole ne mu ki jin tsoronsa. Yesu na tare da mu domin ya bamu salama a duk lokacin wahala.

HOTO NA 35: Mutuwa

HOTO NA 35: Mutuwa

1 Tassalunikawa 4:13-14, 5:9-11; Ruyata Yohana 14:13

Dukanmu mun san cewa wata rana zamu mutu. Amma me zai faru da mu a lokacin? Littafi Mai Tsarki (maganar Allah) ta ce idan mai bi ya mutu, ruhunsa zai je wurin Ubangiji Yesu Almasihu. Kada abokai su yi bakin ciki da yawa. Kada mu ji tsoron mutuwa saboda mun san cewa Allah yana kaunarmu kuma ya cece mu daga zunubi. Marasa bangaskiya ba su da wannan bege mai dadi na rayuwa tare da Allah bayan sun mutu, zasu tafi wurin azaba. Ina zaka tafi idan ka mutu?

HOTO NA 36: Jikin Kristi

HOTO NA 36: Jikin Kristi

Afisawa 4:4-16; 1 Korinthiyawa 12:12-27

Kowanne sashi na jikin mu yana da aikinsa. An yi ido domin gani, kune don ji, baki kuma domin yin magana da cin abinci. Dukan sassa na jiki na yin aiki tare. Idan wani sashi ba shi da lafiya ko in ya ji ciwo (rauni) dukan jiki ne yake shan wahala. Allah ya ce masubi sassan jiki daya ne (wanda ake kira ikilisiya). Yesu ne shugaban wannan jikin. Allah na da aikin da kowanne mai bi zai yi (misali, wa'azi da raira waka da koyarwa da noma da dai sauransu). Dole kowa ya yi aiki domin Ubangiji Yesu domin a taimaki dukan jiki ya yi karfi. Dole masu bi su kaunaci junansu su kuma yi aiki tare in kuwa ba su yi haka ba, jikin Kristi zai sha wahala.

HOTO NA 37: Taruwa domin yin sujada

HOTO NA 37: Taruwa domin yin sujada

Ibraniyawa 10:23-25; Kolosiyawa 3:15-17; 1 Korinthiyawa 11:23-34

Ya kamata masu bi su rika tattaruwa tare suna bautar Allah. Mu koya daga maganar Allah (Littafi Mai Tsarki) ta wurin raira waka da yin addu'a, mu rika kawo kyautai domin aikin Allah. Allah kuma ya umurce mu mu tuna da mutuwar Ubangiji Yesu. Anan mun ga masu bi (mutanen Allah) suna kakarya gurasa da kokon jibi (ana amfani da na gargajiya). Gurasar na yi mana tuni game da jikin Yesu wanda ya bayar akan giciye domin mu. Ruwan na yi mana tuni game da jinin Yesu wanda ya zubar domin ya cece mu daga zunubi.

HOTO NA 38: Yesu zai dawo

HOTO NA 38: Yesu zai dawo

Yohana 14:2-3; 1 Tassulunikawa 4:13 - 5:4

Wata rana ba zato ba tsammani Ubangiji Yesu Almasihu zai dawo daga sama, kamar dai yadda ya alkawarta. Zai dawo ya dauki dukan masu bi na gaskiya (iyalin Alllah). Yesu zai tashe dukan mutanen Allah da suka mutu. Ba za a sami komai a cikin kabarinsu ba. Mutanen Allah da suke da rai zasu tafi tare da su. Dukanmu zamu hadu tare da Ubangiji Yesu a sararin sama mu kuma kasance tare da shi har abada. Za a bar marasa bi a baya domin su fuskanci shari'ar Allah. Ba mu san lokacin da Yesu zai dawo ba, amma mu zauna da shiri. Ko kana shirye ka sadu da Ubangiji Yesu idan ya dawo yau?

HOTO NA 39: Bada ’ya’ya

HOTO NA 39: Bada ’ya’ya

Matta7:15-20; Yohana 15:1-16; Galatiyawa 5:22-23

Kamar yadda itace a cikin wannan hoton yake bada 'ya'ya, haka mai bi (krista) ya ke bada 'ya'ya na ruhaniya. Yesu ya ce "Ni ne itacen inabi, ku ne rassan, idan kun zauna a ciki na, ni kuma a cikin ku, zaku bada 'ya'ya sosai. Ruhu Mai Tsariki na Allah yana zaune a cikin mu yana kuma yin aiki a cikin mu domin bada 'ya'yan kauna da murna da salama da hukuri da jinkai da nasiha da nagarta da aminci da tawali'u da kanewa. Idan rassan itace ba sa bada 'ya'ya, sare su ake yi sai su mutu a kuma kone su. Ana son masu bin Yesu su bada 'ya'ya mai yawa kuma wannan na daukaka sunan Allah Ubangijinmu wanda yake cikin sama.

HOTO NA 40: Yin bishara

HOTO NA 40: Yin bishara

Matta 28:16-20; Markus 16:14-20; Ayyukan Manzani 1:8

Yesu ya umurci dukan masu bi (krista) su je su fadawa dukan mutane wannan labarin mai dadi cewa, zasu sami ceto daga zunubi da gidan wuta. Wannan hoton na nuna mai bi na yin biyayya ga Yesu yana kuma fadawa mutane labarin Yesu. Ruhu Mai Tsariki na Allah zai taimakemu ya bamu karfi wajen yin shaida domin Yesu Almasihu. Ka bayyanawa sauran mutane game da abin da ka koya daga cikin wannan littafi na hoto.

Lotutako informazioa

Free downloads - Here you can find all the main GRN message scripts in several languages, plus pictures and other related materials, available for download.

"Good News" audio-visual - This audio visual set has 40 pictures to present an overview of the Bible from Creation to Christ. It covers the salvation message and basic teaching on the Christian life. It is available in more than 1300 languages.

How to use GRN Audio visual resources - 1: Sharing the Gospel made easy - This article gives an introduction to some of the many different ways the GRN audio visual resources can be used in ministry.

How to use GRN Audio visual resources - 2: Going Deeper - This article gives further explanation of how people learn from the stories, and why the stories do not have a lot of commentary.

The GRN Audio Library - Evangelistic and basic Bible teaching material appropriate to the people's need and culture in a variety of styles and formats.

Choosing the audio or video format to download - What audio and video file formats are available from GRN, and which one is best to use?

Copyright and Licensing - GRN shares it's audio, video and written scripts under Creative Commons

Creating DVDs using the GRN Slide show Videos - How to burn DVDs for specific people groups you are trying to reach