unfoldingWord 27 - Labarin Basamare Nagari
Outline: Luke 10:25-37
Script Number: 1227
Language: Hausa
Audience: General
Genre: Bible Stories & Teac
Purpose: Evangelism; Teaching
Bible Quotation: Paraphrase
Status: Approved
Scripts are basic guidelines for translation and recording into other languages. They should be adapted as necessary to make them understandable and relevant for each different culture and language. Some terms and concepts used may need more explanation or even be replaced or omitted completely.
Script Text
Wata rana, wani masanin shari'ar Yahudawa, ya zo wurin Yesu domin ya gwada shi, yana cewa, "Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?" Yesu ya amsa, "Me aka rubuta a shari'ar Allah?"
Gwanin a dokokin Allah ya ce, "Ku kaunaci Ubangiji Allahn ku da dukkan zuciyar ku, da ran ku, da karfin ku, da kuma hankalin ku. Ka kuma kaunaci, makwabcin ka kamar kanka." Yesu ya amsa, "Ka yi dai dai! Ka yi haka za ka rayu."
Amma masanin shari'ar ya so ya tabbatar shi mai adali ne, sai ya sake yin tambaya, "Wanene makwabci na?"
Yesu ya amsa wa masanin shari'ar ta wurin bada labari. "An yi wani Bayahude da yake tafiya akan hanya daga Urushalima zuwa Yariko."
“Yayin da mutumin yake tafiya, 'yan fashi suka fada masa. Suka kwace duk abin da ye ke da shi, suka kuma yi masa duka har ya kusa mutuwa. Sa'anna suka yi tafiyar su.”
“Nan da nan bayan haka, wani Firist Bayahude tafiya ta kawo shi wannan hanyar. Da wannan shugaban adini ya ga mutumin da aka yi wa duka da fashi, sai ya bi gefe daya na hanyar, ya kyale mutumin nan dake bukatar taimako, ya ci gaba da tafiya.''
"Jim kadan da yin haka, wani Balawe ya gangaro kan hanyar. (Lawiyawa sune kabilun Yahudawa wandanda ke taimakon firistoci a Haikali.) Balawen shima ya ketare gefen hanya, bai kula mutumin da haka yi wa fashi da duka ba.”
“Mutumin da ke biye akan hanyar kuwa Basamare ne. (Samariyawa sune zuriyar Yahudawa wadan da suka auri mutane daga wassu al'umma. Samariyawa da Yahudawa sun tsani juna.) Amma da Basamaren ya ga Bayahuden, ya yi juyayi domin sa. Sai ya lura da shi ya daure masa raunukansa.”
“Basamaren ya dauki mutumin nan ya sa akan jakin sa, ya kai shi wani masauki baki kusa da hanya inda ya kula da shi.”
Kashegari, Basamaren yana bukatar yaci gaba da tafiyar sa. Sai ya ba wa mai kula da masaukin kudi yace, 'Ka lura da shi, idan kudin da kashe yafi wannan, zan biya ka idan na dawo.'''
Sa'annan Yesu ya tambayi masanin shari'ar, "Me kake tunani? A cikin mutanen nan uku, wanene makwabcin wanda aka yi wa fashi da duka?" Sai ya amsa. "Wanda ya yi masa jinkai." Yesu ya gaya masa, "Kaima jeka kayi haka."