unfoldingWord 29 - Labarin Bawa Marar Jinkai
Περίγραμμα: Matthew 18:21-35
Αριθμός σεναρίου: 1229
Γλώσσα: Hausa
Κοινό: General
Σκοπός: Evangelism; Teaching
Features: Bible Stories; Paraphrase Scripture
Κατάσταση: Approved
Τα σενάρια είναι βασικές οδηγίες για μετάφραση και ηχογράφηση σε άλλες γλώσσες. Θα πρέπει να προσαρμόζονται όπως είναι απαραίτητο για να είναι κατανοητές και σχετικές με κάθε διαφορετική κουλτούρα και γλώσσα. Ορισμένοι όροι και έννοιες που χρησιμοποιούνται μπορεί να χρειάζονται περισσότερη εξήγηση ή ακόμη και να αντικατασταθούν ή να παραλειφθούν εντελώς.
Κείμενο σεναρίου
Wata rana, Bitrus ya tambayi Yesu, "Maigida, sau nawa zan yafe wa dan'uwa na, idan yayi mani laifi? Har sau bakwai?'' Yesu ya ce, "Ba sau bakwai ba, amma saba'in sau bakwai!" Ta haka Yesu, na nufin mu rika yafewa a kowone lokaci. Daga nan Yesu ya bada wannan labarin.
Yesu ya ce, "Mulkin Allah na kama da wani sarki wanda yana son ya daidaita ajiyarsa da barorinsa. Daya daga cikin barorin sa na da bashi mai yawan kimanin albashin shekara 200,000."
“Tunda baran ba zai iya biyan bashinsa ba, sarkin ya ce, 'Ku sayar da mutumin nan da iyalinsa su zama bayi don a sami kudin biyan bashin sa."'
"Baran ya fadi kan gwiwarsa a gaban sarkin ya ce, 'Ka yi mini hakuri zan biya ka dukkan kudin ka da yake na.' Sarkin ya ji tausayin baran, ya share duk bashin sa ya sake shi, ya tafi.”
“Amma da baran nan ya fita daga wurin sarkin, ya ga wani bara dan'uwan sa da yake binsa bashi na misallin albashin wata hudu. Baran nan ya damke dan'uwan sa ya ce, 'Ka biya ni kudin da nake binka!'”
“Dan'uwan sa baran ya fadi akan gwiwar sa, ya ce, 'Ka yi hakuri da ni, zan biya dukkan kudin da kake bi na.' Amaimakon haka baran nan ya jefa dan'uwan sa, kurkuku sai lokacin da zai iya biyan duk kudin da yake binsa.”
“Da wasu barorin sun ga abinda ya faru suka damu kwarai. Suka je wurin Sarki suka gaya masa abin da ya faru.”
“Sarkin ya kira baran ya ce, 'Kai mugun bara! Na yafe maka bashin ka, don ka rokeni. Ai da kaima kayi masa haka.' Sarki ya yi fushi ya kama bawan ya jefa mugun bawan cikin kurkuku har sai ya iya biyan duk kudin da yake bin sa.”
Sa'annan, Yesu ya ce, "Haka Ubana na sama zai yi wa kowane dayan ku, idan ba ku yafe wa dan'uwan ku daga cikin zuciya ba."